23 Yuli 2026 - 09:08
Source: ABNA24
Yeman Ta Kai Hari Kan Jiragen Ruwan Dakon Mai Na Saudiyya

Sojojin Yemen sun sanar da cewa, a wani aikin soji, sun kai hari a kan jiragen ruwan dakon mai na Saudiyya guda biyu a Bahar Maliya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Nakalto daga gidan talabijin na "Al-Masirah," Yahya Saree, mai magana da yawun sojojin Yemen, ya bayyana cewa, a wani aikin soji, an kai hari a kan jiragen ruwan dakon mai na Saudiyya guda biyu — "ENCELIA" da "LAYLA" — a Bahar Maliya.

A cikin sanarwar sojojin Yemen an bayyana cewa, an kai hari a kan waɗannan jiragen ruwan dakon mai guda biyu sakamakon keta dokar hana zirga-zirgar ruwa a Bahar Maliya.

Mai magana da yawun sojojin Yemen ya kuma bayyana cewa, an gudanar da aikin ne ta amfani da makamai masu linzami na ballastic, makamai masu linzami na cruise da jirage marasa matuka, kuma kai hari daidai inda aka nufa ya haifar da gobara a kan jiragen ruwan dakon mai guda biyu.

A ci gaban sanarwar yayi ishara da cewa, a wannan aiki, an tilastawa jiragen ruwa kusan 10 ja da baya su koma.

Mai magana da yawun sojojin Yemen ya kuma jaddada cewa, ayyukan ruwa a kan Saudiyya za su ci gaba don aiwatar da ma'aunin "killacewa a kan killacewa."

A ƙarshe, Saree ya yi gargadin cewa, duk wani mataki ko hari daga Saudiyya a kan Yemen, za a fuskance shi da babban aiki a cibiyar ƙasar Saudiyya.

……………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha